Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Najeriya (Nigerian Correctional Service) ta ɗauki matakin ladabtarwa kan wasu jami'ai uku bayan da wani fursuna ya yi amfani da wayar salula ba tare da izini ba a Gidan Yarin Tsaro na Matsakaici da ke Ibara a birnin Abeokuta, Jihar Ogun.

A cikin wata sanarwa, Jami'ar Hulɗa da Jama'a ta Hukumar, Jane Osuji, ta ce binciken farko ya tabbatar da cewa fursunan, wanda ke jiran aiwatar da hukuncin kisa, ya mallaki wayar salula ba bisa ƙa'ida ba, inda ya riƙa amfani da ita wajen shiga shafukan sada zumunta yayin da yake tsare.

Sanarwar ta bayyana cewa an ƙwato wayar, sannan aka mayar da fursunan zuwa wani gidan yari mai tsauraran matakan tsaro, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Hukumar ta kuma ce Babban Kwanturola Janar na Gidajen Yari, Sylvester Nwakuche, ya ba da umarnin cire jami'in da ke kula da Gidan Yarin Ibara tare da wasu manyan jami'ai biyu daga mukamansu nan take, har sai an kammala bincike.

Hukumar ta tabbatar wa 'yan Najeriya cewa duk wanda bincike ya nuna yana da hannu wajen taimakawa ko sauƙaƙa wannan keta tsaro zai fuskanci hukuncin ladabtarwa da matakan gudanarwa kamar yadda dokokin hukumar suka tanada.