Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da cewa an ceto mutane 176 da ƴan bindiga suka sace a harin da suka kai kan al'ummomin Woro da Nuku da ke ƙaramar hukumar Kaiama a farkon watan Fabrairu.

A cikin sanarwar da gwamnatin ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Laraba, ta bayyana godiyarta ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, hukumomin tsaro da kuma duk waɗanda suka ba da gudummawa wajen ganin an samu nasarar ceto mutanen.

A ranar 3 ga Fabrairu ne wasu ƴan bindiga suka kai hari kan ƙauyukan Woro da Nuku, inda suka kashe fiye da mutane 75, sannan suka yi awon gaba da aƙalla mutane 175, lamarin da ya jefa al'ummomin yankin cikin jimami.

Sanarwar gwamnatin ba ta bayyana cikakken bayani kan yadda aka gudanar da aikin ceto ko kuma ko an biya kuɗin fansa kafin sakin mutanen ba.

Wannan ci gaba na zuwa ne makonni kaɗan bayan sakin ɗalibai da malamai 44 da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo, bayan sun shafe sama da makonni bakwai a hannun masu garkuwa da mutane.

Sai dai har yanzu, wasu ɗalibai da malamansu da aka sace a Askira/Uba da ke Jihar Borno na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa, yayin da iyalansu da hukumomin tsaro ke ci gaba da fatan samun nasarar kuɓutar da su.