Mahukuntan Kuwait sun ba da umarnin rufe makarantar ƴan Iran guda ɗaya tilo da ke ƙasar, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan rikicin Gabas ta Tsakiya.
Wata majiya daga Ma'aikatar Ilimi ta Kuwait ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an bayar da umarnin rufe makarantar, sai dai ba ta bayyana takamaiman dalilin da ya sa aka ɗauki wannan mataki ba.
Kuwait na daga cikin ƙasashen yankin Tekun Fasha da Iran ta kai wa hare-hare a lokacin rikicin, sakamakon kasancewar sansanonin sojojin Amurka a ƙasar.
A cewar takardar umarnin Ma'aikatar Ilimi da AFP ta gani, Ministan Ilimi ya amince da soke lasisin makarantar mai zaman kanta ta Iran tare da rufe ta gaba ɗaya.
Sakamakon wannan mataki, an dakatar da karɓar sabbin ɗalibai domin shekarar karatu mai zuwa, yayin da aka umarci iyaye da su mayar da ƴaƴansu zuwa wasu makarantu domin ci gaba da karatunsu.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, hukumomin Kuwait ba su fitar da ƙarin bayani kan dalilan rufe makarantar ba, kuma ba a samu wata sanarwa daga gwamnatin Iran kan lamarin ba.