Gwamnatin Jihar Kano ta amince da dakatar da dukkan ayyukan Shirin Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro a faɗin jihar nan take, domin tabbatar da gaskiya, riƙon da ingancin yadda ake aiwatar da aikin.


Hakan na cikin wata Sanarwa da mai magana da yawun Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano Nabilisi Abubakar Kofar Na'Isa ya sanyawa hannu.


Matakin ya biyo bayan Rahoton babban kwamitin bincike da aka ba alhakin gudanar da cikakken nazari kan yadda aka tsara shirin, da yadda aka rarraba magunguna da kuma yadda aka aiwatar da ayyukan SMC a Jihar Kano.


A cewar wata sanarwar da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta fitar, dakatarwar ta fara aiki nan take, domin bai wa kwamitin damar gudanar da cikakken bincike kan yadda ake tafiyar da shirin, dan gano takardunsa tasirin aikin, bayanan ma’aikata da sauran dukkan ayyukan da suka shafi aiwatar da shirin.


Zuwa yanzu an dakatar da dukkan ayyukan da ake gudanarwa a a cikin gari na rarraba magunguna da wayar da kan al’umma ƙarƙashin shirin SMC har sai an kammala binciken.


Haka kuma, an dakatar da Manajan Shirin daga aiki nan take, yayin da aka miƙa ragamar gudanar da shirin na wucin gadi ga babban jami’i na shirin domin tabbatar da ci gaba da ingantaccen tsari yayin gudanar da binciken.


Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamitin ƙwararru wanda ya ƙunshi shugabannin manyan hukumomin lafiya na jihar. Kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin


Dr. Usman Bashir, Darakta Janar na Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano (SACA),

Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Jihar Kano (SPHCMB) da sauransu.