Gwamnatocin Najeriya da Jamhuriyar Benin sun ƙaddamar da wani sabon shirin haɗin gwiwar tsaro domin ƙarfafa yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da ke barazana ga yankunan iyakokin ƙasashen biyu.

Matakin ya biyo bayan ƙaruwar matsalolin tsaro a yankin, inda ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi suka fara bazuwa daga yankin Sahel zuwa ƙasashen da ke gabar tekun yammacin Afirka.

Shirin haɗin gwiwar na da nufin hana ƴan ta'adda amfani da iyakokin ƙasashen biyu wajen tserewa, sake haɗa ƙarfi ko kai hare-hare.

A ƙarƙashin wannan tsari, rundunonin tsaron Najeriya da Benin za su riƙa gudanar da sintiri da samame na haɗin gwiwa a dazuzzukan da ke kan iyakokin ƙasashen, tare da musayar bayanan sirri cikin gaggawa domin gano tare da fatattakar masu aikata laifuka.

Rahotanni sun nuna cewa ƙaruwar hare-haren ta'addanci tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025 ta sa ƙasashen biyu suka fahimci cewa ba wata ƙasa kaɗai da za ta iya shawo kan wannan barazana ba tare da haɗin kan maƙwabtanta ba.

A wani ɓangare kuma, gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin kafa sabon ɓangaren soji na musamman a yankunan da ke kusa da iyakokin, domin kare wuraren da suka fi fuskantar barazana, musamman dajin Kainji da sauran dazukan da ake zargin ƴan ta'adda na ƙoƙarin mayar da su mafaka.

Ana sa ran wannan mataki zai kuma taimaka wajen dakile safarar makamai ba bisa ƙa'ida ba tsakanin ƙasashen biyu.

Haɗin gwiwar ya fi mayar da hankali kan yaƙi da ƙungiyoyin JNIM, mai alaƙa da Al-Qaeda, da kuma ISWAP, mai alaƙa da Da'esh, waɗanda ake zargi da amfani da garkuwa da mutane, fasa-ƙwauri da yaudarar matasa wajen ci gaba da ayyukansu.

Masana na ganin wannan sabon shiri na iya taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro ba kawai a iyakokin Najeriya da Benin ba, har ma a faɗin yankin yammacin Afirka.