Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da tukuicin kuɗi har naira miliyan 60 ga duk wanda ya bayar da sahihan bayanan da za su kai ga cafke wasu manyan jagororin ƙungiyar ISWAP da ke aiki a yankin Tafkin Chadi.
Sanarwar ta ce an gano mutanen ne bayan binciken ƙwararru da aka yi kan na'urorin sadarwa da kyamarar bidiyo da dakarun Operation Hadin Kai suka ƙwato a wani farmaki da ya hallaka babban mai ɗaukar bidiyo da yaɗa farfaganda na ƙungiyar.
Jami'in Yaɗa Labarai na Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas, Kyaftin Muhammed Goni, ya bayyana cewa binciken ya taimaka wajen gano sansanonin ƴan ta'addan da kuma manyan kwamandojinsu da ke aiki a yankin Mangari–Metele–Dogon Chukun, cikin ƙananan hukumomin Abadam da Kukawa na Jihar Borno.
Daga cikin waɗanda ake nema akwai Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa, wanda aka fi sani da Wali, kuma ake zargin shi ne gwamnan ISWAP a yankin Tafkin Chadi. Haka kuma akwai mataimakinsa, Amirul Jaish Muhammad Jidda, wanda ake yi wa laƙabi da "Mai Hannu Ɗaya", da kuma Hamad Abu Hanifa, wanda ake zargin shi ne Amirul-Fiya na ƙungiyar.
Rundunar ta bayyana Abu Musa a matsayin jagoran ƴan ta'addan da ake nema ruwa a jallo a yankin a halin yanzu.
A cewar sanarwar, an ware naira miliyan 50 ga duk wanda bayanansa za su kai ga cafke Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa, yayin da aka ware naira miliyan 10 kan Muhammad Jidda, lamarin da ya kai jimillar tukuicin zuwa naira miliyan 60.
Sojojin sun tabbatar da cewa za a kiyaye sirrin duk wanda ya bayar da sahihan bayanai, tare da yin kira ga jama'a su ci gaba da bai wa jami'an tsaro haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wani bayani mai amfani ta hanyoyin da aka tanada ko kuma ta lambar waya 0708 498 8859.
Sai dai rundunar ta gargaɗi jama'a da kada su yi ƙoƙarin tunkarar ko kama waɗanda ake nema da kansu, domin su bar aikin ga jami'an tsaro.