Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, ya bayyana cewa yana kallon Iraniyawa a matsayin mutane masu taurin kai, yana mai cewa hakan na daga cikin manyan ƙalubalen da ke hana samun sauƙin warware rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran.
A wata hira da ya yi da tashar Fox News, Vance ya mayar da martani kan sukar da wasu 'yan Amurka ke yi game da yadda gwamnatin ƙasar ke tafiyar da rikicin da Iran.
Ya ce gwamnatin Iran na fuskantar rarrabuwar kawuna, inda wasu daga cikin shugabanninta ke goyon bayan ci gaba da tattaunawa da Amurka, yayin da masu tsattsauran ra'ayi ke son a ci gaba da rikici.
Vance, wanda ya jagoranci tawagar Amurka a tattaunawar da aka gudanar a Islamabad, ya bayyana kwarin gwiwar cewa a ƙarshe za a samu mafita da za ta kasance cikin muradun al'ummar Amurka.
Sai dai ya amince cewa rikicin na ci gaba da fuskantar sauye-sauye, inda ake samun ci gaba a wasu lokuta sannan kuma koma baya a wasu.
A wani bangare kuma, wasu rahotanni sun nuna cewa shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, na iya kai ziyara Pakistan cikin 'yan kwanaki masu zuwa, amma har yanzu gwamnatin Iran ba ta tabbatar ko musanta wannan rahoto ba.