Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliya a wasu yankunan da ke da ƙarancin tudu, yayin da ta yi hasashen ruwan sama da tsawa a sassa da dama na ƙasar.
A cikin hasashen yanayinta na ranar Laraba, 5 ga Agusta, 2026, hukumar ta buƙaci mazauna yankunan da ke cikin haɗarin ambaliya da su kasance cikin shiri, tare da guje wa bi ta hanyoyin da ruwa ya mamaye domin kare rayuka da dukiyoyi.
A yankin Arewacin Najeriya, NiMet ta ce ana sa ran samun tsawa da ruwan sama a jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina, Kano, Zamfara, Gombe, Bauchi, Taraba da Adamawa.
A Arewa ta Tsakiya, ana hasashen tsawa da ruwan sama da safe a Babban Birnin Tarayya (Abuja) da wasu sassan Plateau da Nasarawa, kafin yanayin ya bazu zuwa wasu jihohin yankin da yammacin rana.
A Kudancin Najeriya, hukumar ta ce za a samu gajimare tare da ruwan sama a wasu yankuna, musamman jihohin Ondo, Ekiti, Oyo, da mafi yawan jihohin Kudu maso Gabas da Kudancin Kudu.
Hukumar ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su rika neman sabbin bayanan yanayi kafin gudanar da zirga-zirgarsu, domin tabbatar da tsaro da ingancin harkokin sufurin jiragen sama.