Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Chile (ANFP) ta amince wa mai tsaron ragar Cape Verde, Vozinha, da ya ci gaba da sanya sunan da aka fi saninsa da shi a bayan rigarsa yayin da yake bugawa ƙungiyar Colo Colo.

Mai tsaron ragar mai shekaru 40 ya rattaba hannu kan kwantiragin watanni shida da Colo Colo a ranar Litinin, bayan ya yi fice a idon duniya sakamakon bajintar da ya nuna a gasar cin kofin duniya.

A bisa ƙa'idodin gasar Liga de Primera ta Chile, ya kamata ɗan wasan ya yi amfani da cikakken sunansa na haihuwa, Josimar Jose Evora Dias, domin dokokin ANFP sun haramta amfani da sunayen laƙabi ko na barkwanci a bayan rigunan wasa.

Sai dai, bayan buƙatar da ƙungiyar Colo Colo ta gabatar, hukumar ta ba da izini na musamman domin Vozinha ya ci gaba da amfani da sunan da ya shahara da shi.

Vozinha ya isa birnin Santiago a ranar Lahadi, inda dubban magoya bayan Colo Colo suka tarbe shi cikin girmamawa. Bayan kwana biyu, ya fara atisaye tare da sababbin abokan wasansa, yayin da ake sa ran zai fara taka leda nan ba da jimawa ba.