Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makarantun Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) ta sanar da cewa sama da ɗalibai miliyan 1.2 sun samu sakamako mai kyau a jarabawar WASSCE ta shekarar 2026.

A cewar hukumar, ɗalibai 1,200,514 daga cikin 1,950,726 da suka rubuta jarabawar sun samu kiredit a aƙalla darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi, wanda ya kai kashi 61.54 cikin 100 na jimillar masu jarabawar.

WAEC ta kuma bayyana cewa ta riƙe sakamakon ɗalibai 167,486 bisa zargin hannu a satar jarabawa, yayin da ba ta bayyana adadin waɗanda suka faɗi jarabawar ba.

Hukumar ta sanar da cewa an fitar da sakamakon jarabawar, tare da umartar ɗalibai da su fara samun PIN da Serial Number ta hanyar tsarin WAEC kafin su iya duba sakamakonsu ta shafin binciken sakamako na hukumar.

Haka kuma, WAEC ta ce ɗalibai za su yi amfani da lambar jarabawarsu da kuma Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) da suka yi amfani da ita lokacin rajista domin tantance bayanansu.

Jarabawar WASSCE ta shekarar 2026 ta gudana ne tsakanin 21 ga Afrilu zuwa 19 ga Yunin 2026, inda kusan ɗalibai miliyan 1.96 daga makarantu sama da 24,200 a faɗin Najeriya suka rubuta jarabawar.